Za A Nada Adam A. Zango Sarkin 'Yan Finafinan Hausa

Ku Tura A Social Media...har an yi gagarumin bikin taya shi murna

Kungiyar masu kallon finanfinan Hausa ta kasa baki daya tana daf da baiwa jarumi Adam A. Zango sarautar 'yan fim din Hausa.

A yayin da RARIYA ta zanta da shugaban riko na kungiyar Fala M. Shareef don jin dalilin su na baiwa Adam Zango wannan sarauta, ya bayyana dalilin da ya sa za su ba Adam Zango sarautar ta kanywood kamar haka; don kasancewar sa mai hakuri, iliminsa mutuncinsa, kyautarsa, biyayyarsa, ibadarsa, yafiyarsa ida an yi masa laifi da kuma daukakarsa. Sannan kuma mawaki ne, makadi ne,furodusa ne, darakta ne, edita ne, jarumi ne, dan rawa ne da dai sauransu.

Fala ya kuma kara da cewa wanan sarautar ba su bada ita dan kuntatawa wani ko wata ba sai dan shine wanda ya kamata a baiwa kuma dama can babu sarki a masana'antar fim.

Fala M. Shariff ya ce "Wannan dalilin ne ya sa muka zauna dan tattaunawa akan wa ya kamata aba. Bayan mun yi haka sai muka ga shine wanda ya cancanta. Sannan wannan sarautar ba mu muka ba shi ba Allah ne ya ba shi.

"Sannan kuma kar ku manta mu ma masu kallo muna da 'yanci akan masu shirya finafinan Hausa. Dalilina shine in ba mu ba za su yi ba saboda su suke shiryawa mu kuma muke siya.

Tuni har wasu masoyan Adam Zango  suka shirya bikin taya shi murnar wannan sarauta da za a ba shi. Inda masoyansa da dama suka halarci bikin cikin shigar sarauta da al'adu wanda aka gudanar a jihar Nasaarawa.

Masoyan na A. Zango sun kuma ce yadda aka ga sun yi a wurin taya murnar haka za su yi a ranar nadin sarautar.

Masoyan Zangon sun kuma kara da cewa daga yanzu ba za su kara bari ana cin zarafinsa da tozarta shi ba, inda suka yi barazanar cewa idan aka kara nuna masa bambanci a masana'antar fim za su dauki mataki.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"