Ta Faru Ta Kare : An Sace Amarya Da Mutum 10 a Jahar Kaduna

Ku Tura A Social Media
A daren shekaran jiya ne wani mummunan al’amari ya afku a garin Birnin Gwari, inda aka yi garkuwa da Amarya da wasu mutum 10.
Amaryar wacce aka dauke ta domin a kai ta dakin mijinta, sun gamu da azal ne bayan da ‘yan bindiga suka tare su, sannan suka yi garkuwa da dukkanin ‘yan tawagar kai amaryar.

Wannan danyen lamarin ya auku ne da misalin karfe 8:00 na dare, wanda ya jefa al’ummar yankin cikin taraddadi da rashin tabbas.

Yayin da ya ke tabbatar da aukuwar lamarin, wani tsohon Shugaban karamar hukuma wanda ya bukaci a sakaya sunan sa, ya ce, masu garkuwar sun jima su na cin karensu ba babbaka a yankin domin ba wanda ya isa ya tunkare su.
A cewar sa, masu garkuwar sun dakatar da motar wacce ke dauke da Amaryar, inda suka yi awon gaba da ita da kuma ‘yan rakiyar ta su goma.
Ya ce, lamarin ya auku a tsakanin kilomita 55 daga garin na Birnin Gwari.


Sai dai rahotanni sun ce, uku daga cikin wadanda aka yi garkuwar dasu sun samu damar arcewa, inda suka dawo garin a jiya da safe.
Hanyar ta Birnin Gwari da ake bi zuwa karamar hukumar Funtuwa ta jima da zama tarko ga matafiya wadanda ke bin hanyar sakamakon ta’asar da masu garkuwar suka jima suna tabkawa.

A wata sabuwa kuma, a ranar juma’ar da ta gabata masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da wani matashi a lokacin da yake tafiya akan Babur dinsa daura da kauyen Uduwa a cikin garin na Birnin Gwari.

Har ila yau, masu garkuwa da mutane, sun yi yi garkuwa da dan Mataimakin Liman na Masallacin kauyen Uduwa, inda suka nemi a basu kudin fansa har naira miliyan uku.
Wani shugaban ‘yan sintiri dake kauyen mai suna Hussaini Iduwa ya tabbatar da aukuwar lamarin, a hirar da aka yi dashi.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, Aliyu Muktar ya bayyana cewar labarin bai riski rundunar ba.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"