Fitsararrun 'Yan Mata Dake shigowa Sana'ar Fim Ne Ke Jawo Mana Zagi' - Jamila Nagudu

Ku Tura A Social Media

A wata hira da tayi da BBC hausa, tauraruwar fina-finan Hausa, Jamila Nagudu ta bayyana cewa wasu bata garin 'yan matane dake shigowa masana'antarsu ne daga waje ke sawa ana yi musu kudin goro ana zaginsu.

Jamila tace zaka ga yarinya ta taso a unguwa bata ganin girman iyayenta da manyan mutane kuma sai tazo masana'antar fim ta samu sa'a a dauketa To anan ma sai ta cigaba da wannan hali nata sai mutane su rika ganin kamar duk 'yan fim haka suke.

Jamila ta bayyana cewa ta taba yin aure kuma tana da da daya.

Jamila ta bayyana cewa "tana taka duk wata rawa da aka bata da kyau ne saboda sai mutum ya dage ya nuna kwazo sannan za'a kirashi jarumi, mutum ba zai taba zama jarumi ba haka kawai",

Ta kara da cewa duk wani abu da aka ga tana kuka akanshi a fim ta tabbata idan ace me kallone aka yiwa irin wannan abu to shima zai iya yin kukan.

Jamila ta kara da cewa yawanci yanzu ba sa'anta a masana'antarsu dan da yawa suna kiranta da anti ko Hajiya,

A karshe tace ta godewa Allah da irin abubuwa da daukakar da ta samu, inda ta bayyana cewa ba kowane jarumine ya samu irin abinda ta samu ba a sana'ar fim.

Me za kuce akan hakan?

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"