Sheik Dahiru Bauchi ya Gargadi Gwamnatin Bauchi Game da yi Wa darika katsalandan

Ku Tura A Social Media
Gidauniyar itaccen malamin islama din nan kuma jagoran darikar tijjaniya a Najeriya watau Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gargadi hukumar dake kula da harkar ilimin bai daya watau Universal Basic Education Board (SUBEB) a turance ta jihar Bauchi game da yi wa makarantun allo na zamani katsalandan.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan dake kula da harkokin yada labarai na gidauniyar Malam Ahmad Muhammad Saka ya fitar inda ya yi hasashen babban rikici idan har hukumar ta dage kan sai ta hana yin wazifa da kuma salatul fatihi a makarantun.sanarwar ta kuma bayyana cewa makarantun da gwamnatin tarayya ta gina a jihar dukkan su an yi su ne saboda darajar Sheikh Dahiru Bauchi din don haka bai kamata ba yanzu kuma gwamnatin jihar ta nemi yi masu shishshigi da katsalandan.

A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ikirarin cewa kiristoci da kuma wadanda suka fito daga kudancin Najeriya ne suka fi shanawa a wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari sabanin yadda 'yan kasar ke tsammani.

Farfesa Osinbajo yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wasu 'yan jarida tare kuma da ma'abota anfani da kafar sadarwar zamani a cikin karshen satin nan a jihar Legas.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"