Ji ka ƙaru : Sirrika Guda Bakwai (7) Da Ya katmata Kowane Musulmi Ya Sani Akan ruwan Zam-Zam

Ku Tura A Social Media
Da sanadin shafin yanar gizo na lifeinsaudiarabia.net, NAIJ.com,hausaloaded.com ta kawo muku wasu sirrika goma da ruwan Zam-Zam ya kunsa da kuma ya dace a ce kowane musulmi ya ribaci ilimin da suke tafe da shi domin yada shi ga sauran al'umma.1. Asalin Ruwan Zam-Zam: Dan Hajara Annabi Isma'il, tsira da aminci su kara tabbata a gare su, ya tsunduma cikin yunwa da kishirwa bayan guzuri ya yanke da mahaifin sa Annabi Ibrahim ya bari.

A sakamakon tausayi da jin kai irin na uwa ga dan ta, ta shiga kai komo tare da hawa da sauka a kan duwatsun Safa da Marwa wajen neman abin da dan ta zai sanya a baka. Bayan wannan kai komo har sau bakwai sai kawai cikin mamaki ta ankare da wani ruwa dake gudana a karkashin inda sawayen dan ta, Annabi Isma'il.

2. Wasu sunaye da ake yiwa ruwan lakabi:  Akan kirayi ruwan Zam-Zam da Maimoona, Shabbaa'a da kuma Murwiya.

3. Karfin jiki: Binciken wani masanin kimiyya na kasar Jamus, Dakta Knut Pfeiffer ya bayyana cewa, kwayoyin halittu na jikin dan Adam su kan zabura da zarar an kwankwadi ruwan Zam-Zam.


4. Amfani: Alfanun ruwan Zam-Zam ba su da iyaka, ya kan biya bukata duk wata niyya da aka sha ruwan domin ta.

5. Kiwon Lafiya: Ruwan Zam-Zam ya kunshi sunadaran Magnesium da Calcium dake kawar da wata cuta mai kwazaba.

6. Tarihi: Tun shekaru sama da 4000 da suka gabata, ruwan Zam-Zam yake ta gudana ba bu kakkautawa.

7. Tsafta: Bincike ya bayyana cewa ba bu wani tsaftaceccen ruwa da zai goga kafada da ruwan Zam-Zam.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"