Auren Mawaki Sa'eed Nagudu Ya Hada 'Yan Fim Wuri Guda Kalli Hotuna

Ku Tura A Social Media

Daga Aliyu Ahmad 

An daura auren fitaccen matashin mawaki kuma jarumin finafinan Hausa Sa'eed Yahaya Abubakar wanda aka fi sani da 'Sa'eed Nagudu'.

Auren wanda aka daura shi a yau Asabar, hazikin matashin mawakin, ya auri sahibarsa ne A'isha Umar Na'iyachi  (Shatu) akan sadaki naira dubu hamsin, inda aka daura auren a Masallacin Murtala da ke unguwar Hausawa a cikin birnin Kano, da misalin karfe 11:00 na safe.

Amarya da Angon daman dai sun dade suna soyayya tsakanin su wadda akalla sun fi shekara 7 a tare. Inda su ka yi alkawarin aure a tsakanin su sai daga baya kuma aka ga mawakin ya auri wata 'yar uwar sa a shekarar da ta gabata. inda har wasu suka rika tunanin ya yaudari A'isha. Ashe komai da lokacin sa.

Tun ranar Alhamis din da ta gabata ne aka soma gudanar da shagulgulan bikin, inda yau za a yi Friends day a Chicken Castle ranar 10th ga Maris

Walima a jiya Juma'a a Batul Event Center, Gandu Bayan Traid Fair, Kano

Sai kuma kamu a Gyadi-gyadi Court Road, a Bala Mamsa Street Dan Amar Close.

Wasu daga cikin 'yan fim da suka halarci bikin sun hada da Ali Nuhu, Usman Mu'azu, Kamal S. Alkali, Ali Gumzak, Garzali Miko, Sanusi Oscar, Alhaji Sheshe, Ali Ibrahim Dawayya, Ahmad Shanawa, Hassana da Hussaina da sauransu da dama.

Muna fatan Allah ya sanya alheri.Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"