Al-Qur'ani shine babban Kundi mai koyar da zaman Lafiya - Buhari

Ku Tura A Social Media
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi nema tare da gargadin 'yan Najeriya akan yin riko da fahimtar dukkanin littafai da Allah Madaukakin Sarki ya saukar wajen fadakarwa tare da wa'azantar da zaman lafiya a tsakankanin al'umma.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jihar Katsina, yayin biki na rufe taron gasar karatun Al-Qur'ani ta kasa da aka gudanar karo na 32 a ranar Asabar din da ta gabata.

Shugaba Buhari yake cewa, ko shakka babu Al-Qur'ani shine babban kundin tsari da ya kunshi duk wani tafarki na rayuwar bil Adama. Kuma littafin Mai Girma ya koyar damu yadda zamu yi gaskiya da kuma adalci a duk mu'amalan mu da ya hadar har wadanda ba musulmai ba.

Ya ci gaba da cewa, "tarihin rayuwar Manzo kuma Annabin mu Muhammadu Sallalahu Alaihi Wassalama ya bayyana cewa, akwai wani lokaci da aka tsananta wa Musulmai, inda suka koma wata Daula ta kafirai a kasar Habasha kuma suka zauna lafiya tare da aminci".


karamin ministan sufuri na jiragen sama, Hadi Sirika, shine ya wakilci shugaba Buhari a wannan taro.

Ya kara da cewa, ya kamata mu riki Al-Qur'ani a matsayin madubin haskaka rayuwar mu ba abin kawata gidajen mu ba.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"