Cristiano Ronaldo Ya fi Kowa a Gasar zakarun Turai

Ku Tura A Social Media
Cristiano Ronaldo na ci gaba da kafa gagarumin tarihi a wasannin da yake yi wa Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai, inda kawo yanzu ya ci wa kungiyar kwallo 101, kuma yana kan hanyar karawa.

Ba ri mu fara da yin maraba da Cristiano Ronaldon cikin jerin 'yan wasan da suka ci kwallo 100 a gasar. Su wane ne gwanayen da ke cikin wannan jeri ? Mutum daya ne tal.
Kwallo biyun da ya ci wa Real Madrid ta farfado ta doke Paris St-Germain da ci 3-1, a wasansu na farko na kungiyoyi 16 na karshe, a ranar Laraba, Ronaldo ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallo sama da 100 a gasar zakarun Turai, a kungiya daya.
Dan wasan na gaba a yanzu ya ci kwallo 21 a wasa 12 na karshe da ya yi a gasar ta zakarun Turai, kuma kwallo 11 a wasa bakwai a wannan kakar.

Amma kuma duk da wannan bajinta, wasu mutanen na ganin kokarinsa na raguwa, ya riga ya kai kololuwarsa, yanzu dakushewa yake yi.

To idan aka kwatanta shi da abokan hamayyarsa, ya yake?
Ba shakka Ronaldo zai ji dadin wannan kwatanci. Domin yana da tsiran kwallo hudu da ya ci wa kungiya daya a gasar ta zakarun Turai, tsakaninsa da babban abokin hamayyarsa, Lionel Messi na Barcelona.

Bayan Messi babu ma wani dan wasa da yake kusa da bajintar ta Ronaldo wajen daga raga a gasar ta zakarun Turai.
Ga jadawalin sunayen 'yan wasa da kwallayen da suka ci wa kungiya daya a babbar gasar ta Turai;

1-Cristiano Ronaldo Real Madrid 101
2-Lionel Messi Barcelona 97
3-Raul Real Madrid 66
4-Alessandro del Piero Juventus 42
5-Karim Benzema Real Madrid 41
6-Thomas Muller Bayern Munich 40
7-Didier Drogba Chelsea 36
8-Ruud van Nistelrooy Manchester United 35
9-Thierry Henry Arsenal 35
10-Wayne Rooney Manchester United 30

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"