Aminu shariff Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a birnin Legas

Ku Tura A Social Media


- Sun kwashi 'yan kallon ne a yayin bukin bayar da kyaututtuka na City People Awards

- Aminu Sherif Momoh ne ya lashe kyautar gwarzon jarumin yayin da ita kuma Halima Atete ce ta lashe rukunin jarumai

Fitattun jaruman fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da dama da suka hada da Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a yayin bukin bayar da kyaututtuka na City People Awards da aka saba yi duk shekara.

Mun samu dai cewa Mujallar ta City News da ke zama a birnin Legas ce ke shirya wannan bikin duk shekara inda kuma takan karrama masu ruwa da tsaki a harkar fim na Najeriya kama daga Furodusoshi zuwa jarumai da daraktoci da dai sauran su.

NAIJ.com dai ta samu cewa a bukin mujallar na shekarar 2017, Jamrumi Aminu Sherif Momoh ne ya lashe kyautar gwarzon jarumin yayin da ita kuma Halima Atete ce ta lashe rukunin jarumai na mata.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a watannin baya masana'atar ta Kannywood ta shiga cece-kuce bayan da Jarumi AMinu Momoh ya so ya kunyata jaruma Umma Shehu a yayin wani shiri da yake gabatarwa a gidan Talabijin na Arewa 24.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"