Zaben 2019 INEC ta fitar da ranakun da za'a gudanar da zaben shugaban kasa da na gwamnoni

Ku Tura A Social Media
Hukumar zabe na kasa INEC ta fitar da ranar gudanar da zaben shugaban kasa. Za'a yi zaben ne a ranar asabar 16 ga watan Febreru na 2019.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da haka yayin da ya fitar da kunshin ranaku da shirye shiryen da hukumar tayi na zaben 2019.
Shugaban yace za'a gudanar da zaben gwamnoni a ranar 2 ga watan Maris 2019 a sauran jihohin kasa banda jihar Anambra, Bayelsa, Kogi, Edo, Ondo, Ekiti da Osun.

Bisa bayanin jagoran hukumar za'a gudanar da zaben shugaban kasa da ta yan majalisar tarayya rana guda. Haka kuma, zaben yan majalisar jiha zata wakana rana guda da ta zaben gwamnoni a 2 ga watan maris na 2019.

Hukumar dai ta fitar da ranakun fara yakin neman zaben ga masu takara.
Jam'iyu da masu takarar shugaban kasa da majalisar tarayya zasu fara yakin neman zaben tun daga ranar 18 ga watan Nuwamba na 2018 har zuwa ranar 14 na watan Febreru na 2019.

Hakazalika yan takarar gwamna da majalisar jihohi zasu fara yakin neman kuri'u daga ranar 1 ga watan Disemba zuwa na 2018 zuwa ranar 28 na watan febreru 2019.
Jam'iyu zasu fara amsar takardar takara daga babban ofishin hukumar dake Abuja tun daga ranar 17 na watan Agusta har zuwa ranar 28 na watan Agusta na 2018.
Hukumar dai ta ba jam'iyu damar yin zaben fitar da yan takarar jam'iya tare da magance duk wani matsala da ya taso sanadiyar takarar tsakanin ranar 18 na watan Agusta, 2018 zuwa ranar 7na Oktoba, 2018.

Sources pulse. Ng

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"