Shiyasa Najeriya :PDP na gudanar da babban taronta na kasa

Ku Tura A Social Media
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya na gudanar da babban taronta na kasa, inda za ta zabi shugaban da zai jagorance ta tun bayan rikicin shugabanci na ciki mafi muni da ya so kassara ta a baya-bayan nan.

Karon farko kenan, wakilai kusan dubu uku da aka tantance za su zabi jerin shugabannin jam'iyyar PDP, tun bayan mummunan kayen da ta sha.
Wasu masharhanta dai na cewa samun nasarar babban taron PDP na ranar Asabar ne zai tabbatar da dorewar jam'iyyar har ma ta iya kokarin kwace mulki daga jam'iyyar APC mai mulki a 2019.

Shugaban riko na jam'iyyar PDP, Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ya ce sun tanadi duk muhimman abubuwa don gudanar wannan babban taro kuma tun daga jajiberen ranar taron, an ga 'ya'yan jam'iyyar na dandazon shigowa Abuja.

PDP dai ta ba wa bangaren kudancin kasar damar fitar da shugaban jam'iyyar na gaba, yayin da ake sa rai bangaren arewa zai fitar da mutumin da zai yi mata takarar shugabancin kasa a zaben 2019.

Daga cikin mutanen da suke takarar shugabancin jam'iyyar akwai tsohon Ministan Wasanni da Ayyuka na Musammam, Farfesa Taoheed Adedoja, da Jimi Agbaje wani tsohon dan takarar gwamna a PDP daga jihar Legas.

Sai Cif Raymond Dokpesi mai harkar yada labarai da wani tsohon gwamna a jihar Ogun Gbenga Daniel da wani tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa Bode George wanda rahotanni suke cewa ya janye takararsa daga baya.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa takarar za ta fi zafi tsakanin Farfesa Tunde Adeniran daga shiyyar Kudu maso yamma da kuma Uche Secondus daga shiyyar Kudu maso kudu.

Sanata Makarfi ya ce bangarorin sun zauna sun sake raba mukaman da jam'iyyar ta ba su zuwa shiyyoyi daban-daban, abin da su ba sa ganin haufinsa a siyasance, ko da yake su ba dauke lamarin a matsayin doka ba.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"