Sabon Salo Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Shirya Fim Mai Suna "Yaki A Soyayya"

Ku Tura A Social Media

A kwanakinnan ne Nafisa Abdullahi ta fitar da wani Samfurin wakar Sabon fim dinta mai suna Yaki A Soyayya; fim din wanda kafin yanzu ana kiransa da suna Karma ya hada fitattun Jarumai irinsu Abdul M Shareef, Nafisa Abdullahi, falalu Dorayi, Bilkisu Abdullahi da dai sauransu.

A wata hira da manema Labarai Nafisa ta bayyana cewa kafin shirya fim din sai da Aljihunta ya Girgiza ma'ana ta kashe kudade da yawa, ta kara da cewa fim din ya qara fito da wata baiwa tata wadda ita kanta bata san tana da ita ba sannan ta samu fasahar kirkiro labarin ne yayinda take kallon wani fim, kuma tayi aikin Daukan shirin ne a garuruwan Abuja da Lagos
Nafisa Abdullahi hakika babbar jaruma ce da ta shafe shekaru da dama a masana'antar kannywood ta kuma lashe kyaututtuka masu tarin yawa daga ciki da kuma wajen kasar nan.

Daga karshe ne kuma ta kara tabbatar wa da magoya bayan ta cikakkiyar kaunar ta agare su tare da shan alwashin cigaba da kayatar da su a cikin fina-finan ta.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"