'Mai na iya sauki da zarar an gyara matatun Nigeria'

Ku Tura A Social Media
Kamfanin samar da man fetur na Najeriya NNPC ya ce akwai yiwuwar samun ragin farashin man fetur da ake sayarwa a cikin kasar, idan aka kammala gyara matatun man fetur na gwamnati.

Jagoran kamfanin, Dr. Mai Kanti Baru ya ce yana sa rai da zarar sun samu kudin gyara matatun, kuma suka koma aiki gadan-gadan, a cikin shekara daya da rabi zuwa biyu za a iya kammala gyare-gyaren.

Za a samu bambanci don kuwa akwai kudin kai wa da kawo shi cikin kasar nan, wanda idan a kasar nan aka tace shi, za a samu saukin wadannan kudade a cewar Mai Kanti.
Najeriya dai na shigo da man fetur din da take bukata ne a cikin gida saboda tabarbarewar matatunta, duk da dumbin arzikin mai da take da shi.
Manyan matatun man fetur din gwamnatin kasar sun hadar da na Kaduna da Fatakwal da Warri.

Ya ce: "abubuwan da suka faru a baya ne suka zama sanadin rashin samun isasshen kudin gyara matatun man fetur din kasar."
A cewarsa "Kamar mota ce ta samu matsala", matsalolin kuwa su ne a lokacin da ake kammala gyaran wata, sai a samu wata ta balle.
Mai Kanti Baru ya ce fahimtar da suka yi matsalolin matatun man fetur din, ta hanyar samo masu zuba jari da samar da kudin gyara don mayar da matatun su ci gaba da aiki tamkar sabbi.

Babban manajan daraktan NNPC ya ce a fahimtarsa babu wani zagon kasa da ake yi wa matatun kasar, kamar wasu ke zargi daga ma'aikatan bangaren da wasu 'yan kasuwa.
Ya ce ba kamar a baya ba, yanzu sun tantance dillalan da ke shigo da man fetur daga kasashen waje kuma cikin farashi mai rahusa ta yadda babu wata alaka tsakanin masu shigo da mai da kuma ma'aikatan matatun mai.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"