KYAUTAR BIKIN CHIRISMAS: HALAL KO HARAM? Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Ku Tura A Social Media

-Da yawa musulmi suna tambayar shin ya halatta su karbi kyautar kiristoci a ranar kirsemiti, musamman wadanda suke zaune lafiya tare dasu, ko suke aiki a guri daya. Ga bayaninda malamai sukayi dangane da haka:

1. Ba ya halatta ga musulmi yanuna farincikinsa da wannan ranar, ta hanyar aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamantansu.

2. Ba ya halatta gare shi yaci abinda aka yanka da sunan wannan rana.

3. Ya halatta yakarbi kyautar da zasu bashi a wannan ranar, Kamar yadda ya halatta gare shi yaci abinda za su bashi wadanda ba yankawa akayi ba. Kamar kayan marmari.

Dalili kuwa shine:
A) Baihaqi ya rawaito acikin Littafinsa As-Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad Bin Sirin yace: ankawo wa Ali, Allah yakara yarda agare shi, kyautar idin majusawa Nairuz. Sai yace mene wannan kuma? Sai sukace masa, ya Sarkin Muninai yau ranar idin Nairuz ce. Sai yace, to kullum ma suyi 'Nairuz'. Wato ya karba, tare nuna yaji dadin kyautar.

B) Ibn Abi Shaibah acikin littafinsa Al-Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu Barzata Al-A
slamy cewa: yana da makwabta majusawa, kuma a duk ranar bukukuwansu suna aiko masa da kyaututtuka gidansa, Sai yakan cewa iyalinsa, yaya abin yake?; idan kayan marmari ne to kuci, wanda kuma ba kayan marmari bane, to kumayar musu kayansu.

C) Haka kuma ya rawaito 5/126 cewa, wata mata ta tambayi Nana A'isha tace, muna tare da mata majusawa masu sana'ar shayar da jarirai, to duk ranar idinsu suna aiko mana da kyauta. Sai A'isha, Allah yakara yarda a gareta tace mata, abinda aka yanka domin wannan ranar kada kuci. Kuci kayan marmari na itatuwa.

Ibn Taimiyya yace, wannan ya nuna idinsu ba shi da wani tasiri wajen yahana akarbi kyautarsu. Karbar kyautarsu a ranar da ba idin ba duk hukuncin daya ne domin wannan ba shine taimaka musu ba akan aikinsu na kafirci.

Duba Littafinsa Iqtidha' Siradil Mustaqim 2/52
Sannan akarshe yana dakyau mufahimci cewa, Ba ya halatta musulmi ya taimaka da yi musu yanka a wannan ranar.
Kuma koda mu

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"