Jarumi Adam A Zango Ya Bayarda Dama Ga Duk Masoyansa Mai Son Haduwa Da Shi

Ku Tura A Social Media
Daga: AHMAD SAULAWA, ABUJA.
Saboda haka yake da Dunbin Masoya a duk fadin Nigeria dama duniya baki daya, Dan haka ne ya shirya Ganawa da masoyansa domin cin abincin dare tare dasu ( Dinner ) a garin kano.
A kwankin baya ne Adamu Zango ya saka wata Gasa akan fim dinsa mai fitowa Gwaska return, inda aka dora fiye da Naira dubu Hamsin ga duk wadanda suka ci wannan gasa; daga na daya har zuwa na uku kowa yana da kyauta.

A watannin da suka wuce ne aka fitar da sakamakon Gasar sannan aka saka ranar da za'a basu wannan kyauta, amma har ranar tazo ta wuce ba'a basu ba kuma ba'a ce musu komai ba, wanda hakan yasa akai ta rade-radin cewa dama bazai iya bada wadannan kyaututtuka ba.

Sai a satin da ya Gabata ne Adamun yayi wa wadannan mutane bazata inda ya bayyana Ranar 11 ga watan nan zai shigo garin kano domin yin bikin bada kyaututtuka da kuma Ganawa da masoyansa Guda talatin na cikin garin kano, mata 15 maza 15.
Kamar yanda ya sanar yace idan har mutum zai iya fitowa a bidiyo kuma yana so ya hadu dashi, sai mutum ya tura numbar wayarsa a sakon karta kwana ( message ) a shafin Adamun na Instagram.

Wannan za'a iya cewa wata damace wadda wani Jarumi bai taba bada irinta ba a tarihin kannywood, Adamun yace yasan ba iya kano bane yake da masoya, Dan haka zai zagaya duk fadin arewacin Nigeria wato jihohi Goma sha tara domin yin irin wannan ganawar da masoyansa sai dai ya zabi kano a matsayin itace ta farko.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"