Ta Faru Ta Kare :-Idan kinji haushin rashin aurena ki turo min lambar mahaifin ki - martanin da Maryam Booth ta mayar ma wata da ta nema ta da baƙar maganar

Ku Tura A Social Media


Ita dai wannan Idan kinji haushin rashin maabociyar ta gamu da dodon ta yayin da ta kai bakan magana shafinta

Fittaciyar jarumar masana'antar Kannywood Maryam Booth ta mayar ma wata ma'abociyar shafinta da martani mai radadi bisa ga bakan maganar da tayi.

Lamarin ya faru ne sanadiyar sakon talla da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram na wata garabasa da Jaruma empire wanda ke safarar kayan ma'aurat ke bada wa ga kustomomin ta.

Sako ne ga duk mai son samun garabasa amma wata mai suna @fadeelamatawalle mai bibiyan shafinta tayi mata mummunar fassara.

"Allah ya kyauta ya shirya ki. Ashe duk irin ku daya ne. koda yake yanzu nagan Allah ya fara shiryata tanasa dan mayafi.

jaruma mai naira kuma mai kyautar nairori ashe tana baki kudi?. Ashe kina amsan kaya shiyasa kika kasa aure duk da gorontulan da lakanin nata" . ta rubuta.
Sakamakon abun da ta rubuta jarumar ta mayar mata da martani kamar haka;

" @fadeelamatawalle » Baki da labari? @jaaruma_empire » tana bani kudi kam ba karya.

@fadeelamatawalle » Allah sarki gaki yarinya karama sai uban Shishigility but I don’t blame u I blame tsohuwarki da bata baki tarbiyar “mind ur business ba” ur too young for all this and inkinji haushin rashin aurena DM me ur fathers number".

Suma ma'abotan shafin Maryam ta instagram sunyi tsokaci game da maganar da ita @fadeelamatawalle tayi inda suma suka yi mata zaren mikiya da maganganu.


Yayin da ita dai wannan baiwar Allah ta gamu da uwayen gidan ta wajen yi bakar magana, wasu daga cikin masoyan Maryam Booth na ganin tayi tsanani da irin martani da mayar domin a matsayin ta na jaruma wanda ake koyi da ita bai kamata ta biye mata ba har ma ta mayar mata da bakar magana.

Hakazalika wasu na ganin bai kamata ta sanya mahaifinta a cikin martanin da ta mayar mata.
Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"