Moppan Ta Fasa Yafewa Rahama Sadau Saboda Dalilai kamar Haka

Ku Tura A Social Media
A mujallar Fim ta watan Nuwamba 2017, an buga babban labari kan badakalar nan ta neman a yafe wa Rahama Sadau a dawo da ita Kannywood.
Yau sama da shekara daya kenan tun da jarumar ta bar masana'antar finafinan Hausa, ta tare a Nollywood.

Mun riga mun ba ku labarin yadda jarumar ta kai wasika ga kungiyar MOPPAN sannan ta yi hira a rediyo inda ta bada hakuri kan rawar cashewa wadda ta yi da mawakin hip-hop din nan ClassiQ a wani bidiyo, wanda ya sa kungiyar ta kore ta daga industiri a watan Oktoba na bara.

A labaran da su ka gabata, mun shaida maku cewa MOPPAN za ta zauna domin duba yiwuwar yafe wa jarumar, har ma yawancin shugabannin kungiyar na so a yafe mata "domin a wuce wajen".

To yaya aka yi kuma kungiyar ta soke batun yafe mata a yanzu?
A cikin labarin akwai bayanin cewa jarumar ta tafi kasar Cyprus da ke nahiyar Turai, kuma za ta shafe watanni kusan uku a can.
Mujallar Fim na dauke da labarin yadda aka yi.

Bayan haka, mujallar na dauke da labarin takaddamar da ta faru tsakanin jaruma Umma Shehu da jarumi Aminu A. Shariff (Momoh) a kan hirar da ya yi da ita a shirin sa na "Kundin Kannywood" wanda ya ke gabatarwa a tashar talbijin ta Arewa24.

Jarumar 'yar Kaduna ta yi hira ta musamman da mujallar Fim kan al'amarin a karon farko, inda ta bayyana yadda ta ji kan caa din da mutane su ka yi mata, su na cewa wai ita jahila ce. Shin ko Umma Shehu ta ga laifin Momoh da ya tsinka ta a bainar jama'a?
Za ku ji ra'ayin wasu 'yan fim kan lamarin, cikin su har da Bello Muhammad Bello (BMB) wanda ya ce shi ya na son a hada shi hira da Momoh ba don komai ba sai don ya yi maganin sa kan yadda ya ce ya na tozarta 'yan fim a shirin nasa.

A cikin mujallar akwai wasu dad'ad'an labaran da hirarraki, ga kuma filin ra'ayoyin jama'a.
Ana saida mujallar a jihohi da dama na Nijeriya, saboda haka ya kamata ku nema ku karanta. Farashin ta N1,000 ne kacal.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"