Guguwar siyasa :- PDP na zawarcin Kwankwaso ya bar APC zata bashi takara 2019

Ku Tura A Social Media


PDP na zawarcin Kwankwaso ya bar APC zata bashi takara 2019
Majiyoyi masu tushe sun ruwaito cewa jigogin jam’iyyar PDP na cigaba da matsawa tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso lamba kan ya bi sahun Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar APC.

Bayanai sun nuna cewa hakan ne ma tasa a kwanakin baya Kwankwaso ya gana da Shugaban PDP na kasa, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi da Abdul Ningi a Kaduna a inda suka tattauna batun makomar siyasarsa.

Kawo yanzu dai bayanai sun nuna cewa jigogin jam’iyyar PDP sun fi raja’a a kan tsayar da Kwankwaso a matsayin dan takarar Shugabancin kasa na jam’iyyar ganin yadda ya karbu a kowane sashin kasarnan fiye da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Suna kuma ganin shine koda jam’iyyar APC ta tsaida Buhari a 2019 Kwankwaso ne kadai dan takarar da zai iya ja da Buharin a 2019 musamman idan akayi la’akari da zaben fidda Gwamni na jam’iyyar APC a 2015 inda mista Kwankwso ya zo na biyu a zaben.

Cikin wadanda suke muradin ganin Kwankwaso ya koma PDP sun hada da shugaban amintattu na jam’iyyar ta kasa, Sanata Walid Jibrin, da tsohon Kakakin jam’iyyar ta kasa Barrister Abdullahi Jalo, da shugaban magoya bayan Kwankwaso, Alhaji Sharu Garba Gwammaja,

Mista Jalo yace yayi fatan Ganin tsohon Gwamnan Kanon ya sauya sheka zuwa PDP tun da wuri domin a tsara abubuwa tun da wuri. A yayinda magoya bayan tsohon Gwamnan ke ganin gwara ma Kwamkwason ya koma PDP domin APC ba zata bashi damar kaiwa ga cimma manufofinsa ba.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"