Falana Ya Sake Rokon Buhari Kan Ya Saukakawa El Zakzaky Kuncin Da Yake Ciki

Ku Tura A Social Media


Fitaccen lauyan nan, Femi Falana ya sake rubutawa Shugaba Muhammad Buhari wasika inda ya roke shi kan ya bayar da umarni a saki Shugaban Kungiyar Shi'a, Malam Ibrahim El Zakzaky saboda ya je kasar waje don a duba lafiyarsa shi da uwargidansa Malama Zainab wadda har yanzu akwai harsashi a jikinta.

A cikin wasikar, Lauyan ya ja hankalin Shugaba Buhari kan cewa El Zakzaky ya rasa idonsa guda kuma a halin yanzu dayan idon na fuskantar barazana kuma iyalansa sun nemi a ba su izini su shigo da kwararren likita daga waje don a duba idon amma kuma jami'an tsaro na DSS sun ki amincewa.

Lauyan ya kara da cewa kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin malamin tare da biyansa diyyar Naira Bilyan 50 amma kuma gwamnatin tarayya ta ki mutunta wannan hukuncin kotun inda ya nuna cewa hakan zai sa a dauki gwamnatin a matsayin wadda ba ta mutunta tsarin doka.

Rahoto:- Daga Rariya

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"