Dukkanin Malaman Firamare Da El Rufa'i Ya Kora, Su Zo Zan Ba Su Aiki A Kamfani Na, Inji Alhaji Aminu, Shugaban Kamfanin Bizi Mobile

Ku Tura A Social Media

Daga Ibrahim Ammani Kaduna 

An bukaci dukkanin Malaman Firamare Dubu Ashirin da biyu wadanda Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Nasiru El Rufa'I ta kora a kwanakin baya da cewar, su kwantar da hankalin su kayan su sun tsinke a gindin kaba, domin Kamfanin Bizi Mobile da ke hada hadar Kudi ta Bankuna ya shirya tsaf domin daukar su aiki nan take cikin kwanciyar hankali. 

Wannan albishir din ya fito ne daga bakin Shugaban Kamfanin Bizi Mobile na kasa baki daya Alhaji Aminu Aminu, lokacin da yake jawabi a yayin wani taron manema labarai da Kamfanin ya kira, wanda ya gudana a gidan Jaridar New Nigeria dake kan Titin Ahmadu Bello tsakiyar garin Kaduna. 

Shugaban Kamfanin ya kara da cewar, babu mai bashi tausayi a rayuwar shi irin Ma'aikacin Gwamnati wanda ke jiran wata ya kare ya amshi albashi, saboda duk mutumin da Allah ya nufa ya shigo da'irar Bizi Mobile, babu shakka dole yayi bankwana da dukkanin wani aiki da za'a lashe kwanaki 30 kafin a biya, idan har amma biya kudin kenan. Saboda haka tsarin Bizi Mobile tsari ne wanda ya baiwa Ma'aikatan shi damar yin harka kai tsaye da kudade ta Bankuna, kuma tsarin ya yadu ya zuwa kowane lungu da sako na kasar nan, musanman idan babu Bankuna, 'yan kasuwa da sauran jama'a masu harkokin hada hadar kudi za su iya samun wakilan Bizi Mobile su cire kudaden su ta hanyar amfani da na'urar fitar da kudi, da biyan kudin da bai taka Kara ya karya ba na ladar fitar da kudaden da aka cire. 

Alhaji Aminu Aminu ya tabbatar da cewar za su samar da gurabun ayyuka ga Matasa Miliyan biyu wadanda suka kammala karatu babu aiki daga nan zuwa Watan Maris na shekarar 2018, saboda haka kofa a bude take ga kowa da kowa wadanda ke bukatar yin bankwana da talauci da su rungumi wannan tsari na Bizi Mobile, wanda rassan Kamfanin ke ko ina a fadin kasar.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"