Bamu Ci Kudin Makamai Ba Inji Kungiyar Izala Daga Sheikh Kabiru Hauruna Gombe

Ku Tura A Social Media
Daya daga cikin jagororin Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Gombe, ya musanta zargin da ake wa kungiyar kan karbar "kudin makamai".

Ana zargin gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da raba wa jama'a da kungiyoyi da kuma kamfanoni a kasar makudan kudin da aka ware don sayo wadansu makamai.

Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis tare da rakiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau, wanda shi ne shugaban kungiyar JIBWIS.

"Ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da maganar karbar kudin makamai. Wannan abu ne da kungiyar Izala ba ta taba shiga cikin shi ba," in ji Sheikh Kabiru Gombe.
Gwamnatin Najeriya tana ci gaba da tsare tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki ne bisa zargin yana da hannu a badakalar kudin sayo makamai da suka kai dala biliyan biyu.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"