An kama 'yan gidan sarautar Saudiyya 11 kan zargin cin hanci

Ku Tura A Social Media


Wani sabon kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na Saudiyya ya cafke yarimomi 11 da ministoci hudu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An kama su ne sa'o'i kadan bayan kaddamar da kwamitin wanda Yarima Mai Jiran Gado Muhammad bin Salman yake jagoranta.

Yarima Alwaleed bin Talal wanda biloniya ne da ke da hannun jari a kamfanonin Twitter da kuma Apple, yana cikin wadanda aka tsare.

Hakazalika Sarkin Salman ya sauya shugabannin dakarun tsaron kasar da kuma na sojin ruwa.

Sabuwar dokar yaki da cin hancin ta ayyana cewa: "Kasar nan ba za ta dore ba matukar ba mu magance cin hanci da kuma binciken wadanda suke aika ta shi ba."


Yarima Muhammad yana kokarin kara karfin ikonsa ne yayin da yake kara kawo sauye-sauye a masarautar kasar, kamar yadda wakilin BBC kan harkokin tsaro Frank Gardner ya ce.
Sabon kwamitin yana da ikon tsarewa da kuma haramta tafiye-tafiye ga wadanda ake zargi da cin hanci, a cewar kafar yada labaran kasar.

Sai dai ba a bayyana abin da ake zarginsu da aikatawa ba tukuna.

Amma kafar yada labarai ta Al-Arabiya ta ce an fara wani bincike kan ambaliyar ruwan da aka yi a birnin Jeddah a shekarar 2009 da kuma barkewar cutar Mers wadda aka yi a shekarar 2012.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"