Za'a karrama fitattun jaruman fina-finan Hausa 7 a kasar Ingila

Ku Tura A Social Media

Labaran da muke samu ba da dadewa a nan na nuni da cewa wasu fitattun jarumai a masana'antar fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywoood da suka tasamma akalla bakwai za su samu kyautar karramawa a kasar Ingila.

Jaruman dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu wani babban kamfanin jarida ne na African Voice dake da hedikwatar sa a birnin Landan zai karrama zakakuran jaruman a cikin wata mai kamawa na Nuwamba kuma a ranar hudu ga wata.

Hausaloaded.com dai ta samu cewa wadanda jaridar zata karrama sune Nafisa Abdullahi (Jarumar da tafi fice); Hafsat Ahmed Idris (Babbar Jaruma); Halima Atete (babbar mataimakiyar Jaruma); Ramadan Booth (Babban jarumi); Sani Ahmad Yaro (Babban mataimakin jarumi); Kamal Alkali (Fitaccen mai bada umurni); Hamisu Lamido Iyantama (Fitaccen mai shirya fina finai).

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai wasu jaruman a masana'atar ta Kannywood sun amshi kyaututtuka da dama a wani buki da aka gabatar a birnin tarayya Abuja.

Rahito:Naij.com

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"