Ummah Shehu ta fadi gaskiya cewa da tayi ‘Yan wasan yanzu sun fi na da gogewa – Mansurah Isah

Ku Tura A Social Media
Mansurah Isah ta goyi bayan furucin Umma Shehu kan martanin da ta maida wa Ummi ZeeZee

- Umma Shehu tace yan wasan yanzu sun fi na baya gogewa

- Munsurah tace bata ga wani abin jayayya a kai ba

Tsohuwar Jaruma, kuma shahararriya a dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood Mansurah Isah ta goyi bayan furucin Umma Shehu kan martanin da ta maida wa Ummi ZeeZee na cewa yan wasan yanu sun fi na baya gogewa.

Mansurah wace ta kasance mata ga wani jigo na masana’antar shirya fina-finan wato Sani Musa Danja ta fadi haka ne a wani hira da tayi da wakilin Premium Times a Abuja in da tace ita bata ga wani abin jayayya a kai ba.


Ummah Shehu ta fadi gaskiya cewa da tayi ‘Yan wasan yanzu sun fi na da gogewa – Mansurah Isah
A cewar ta: “ Idan ka duba yanzu jarumai na wannan zamani na samun cigaba, sannan kuma an samu cigaba a harkar kimiyya da fasaha da kuma kimiyyar yanar gizo. Ba za’a taba hada zamanin mu ba inda zaka wani fim din ma a wajen daukar sa ne ake gaya wa jarumi abin da zai yi ko fadi."Yanzu kuwa za’a baka shi a rubuce kayi ta bita har zuwa ranar da za’a fara daukar fim din. Sannan akwai kwarewa yanzu ba kamar da ba. Saboda haka ba zaka ha daba.

“Wasu daga cikin wadanda muka yi zamani da su har yanzu suna damawa a fagen fim din amma dai ai kai kanka ka san ba za su iya hada kansu da masu tasowa ba sai dai su taka iya rawar ganin da zasu iya. Musamman mu mata da muke da kaiyadadden lokacin haskawa a rayuwa gaba dayan ta.”

Ta yabawa jaruman wannan lokaci da yin kira garesu da su mai da hankali a sana’ar domin ganin kannywood ya ci gaba.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"