'Yan PDP ne rabin gwamnatin Buhari – Hameed Ali

Ku Tura A Social Media
Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya Kanar Hameed Ali ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa cika alkawurran da ta yi wa al'ummar kasar na kawo sauyi.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi lokacin kaddamar da wani sabon ofishin kungiyar goyon bayan Shugaba Buhari wato (Buhari Support Organisation BSO) a Abuja ranar Juma'a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Kungiyar BSO ita ce babbar kungiyar da ta kunshi sauran kungiyoyi da suka shige wa shugaban gaban wajen yakin neman zaben shekarar 2015.


"A yanzu, zan iya cewa muna da 'ya'yan jam'iyyar PDP kaso 50 cikin 100 a cikin gwamnatinmu. Ta yaya za a ci gaba da wannan nauyin a kanmu? Ta yaya za mu iya cimma abin da muke fata da wannan nauyin," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "A yanzu 'yan PDP ne suke ba da umarnin abin da za a yi. Wannan ne abin da ya kamata mu yaka. Za mu yi yaki don kwato hakkinmu da kuma kyawawan manufofin gwamnatinmu."

Hakazalika ya ce lokaci ya yi da za su farka daga bacci don samar wa kasar makoma ta gari.
Sai dai ya ce "Shugaba Buhari ba shi da wata matsala don yana abin da ya dace ne."
Har ila yau ya ce "wadanda suka yi aiki tukuru wajen ganin gwamnatin canji ta kai ga nasara ba a saka musu ba tukuna."

Daga nan ya ce "wajibi ne kungiyar BSO ta tashi tsaye wajen ganin ta jagoranci sabon yakin kawo shugabanci nagari. Dole ne mu yi haka don gyara sunanmu da kuma sunan shugaban kasa da abin da yake yi."
"Shugabanmu yana yin abin da ya dace kuma wajibi ne mu ba shi goyon bayan da yake bukata," in ji shi.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"