Nijeriya vs Argentina Super eagles na shirin karawa da tawagar Lionel Messi a ƙasar Rasha

Ku Tura A Social Media
Hukumar kwallon kafa ta NFF ta sanar cewa tawagar super eagles zata kara da ƙasar Argentina a ranar 14 ga watan Nuwamba a kasar Rasha.

Wannan yana daga cikin wasan shirye-shiryen damawa a gasar waorld cup da za'a gabatar a 2018 wanda Super eagles ta samu nasarar zama kasa ta farko daga nahiyar afrika da shiga gasar bayan wasannin share fage da aka buga.

Cikin jerin wasannin na abokantaka da Super eagles zata buga zata fara da kasar Argentina ranar talata 14 ga watan Nuwamba a birnin

Krasnodar daya daga cikin biranen da za'a buga wasannin gasar World cup a 2018.
A bisa labarin sakateren NFF Dr Muhammed Sanusi wasan Nijeriya da Argentina zata kasance bayan sun samu amincewar hukumar kwallon kafa na duniya wato FIFA.
Sanusi yace NFF ta samu tayi daga ƙasar Iran da
Saudi Arabia da Morocco amma ta zabi
Argentina.

Kafin wasan su da Argentina Super Eagles zata kaya da Kasar Algeria a wasan share fage na gasar World cup karo na karshe.
A wasannin kece raini da ƙasashen suka buga a baya sunyi kunen doki inda Argentina ta ci nasa a daya hakazalika Super eagles ta lallasa su a dayan da aka buga a garin Abuja cikin watan Yuni na 2011.
karawa 4 suka yi a gasar kwallon kafa na duniya da suka yi super eagles ta sha kasa inda dukannin wassanin Argentina ta doke ta.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"