Nigeria: Malamai sun fadi jarrabawar 'yan aji hudu a Kaduna

Ku Tura A Social Media

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na shirin sallamar malamai 21,780 daga cikin 33,000, sakamkon faduwa jarrabawar da aka shirya musu ta matakin 'yan aji hudu don jarraba kwazonsu.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa a yanzu haka jihar Kaduna na neman sababbin malamai guda 25,000, a wani bangaren na shirye-shiryan da take yi don dawo da martabar ilimi a jihar.
Gwamnan jihar Nasir el-Rufai ya gabatar da wannan shirin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Bankin Duniya a Kaduna a ranar Litinin.
''Mun jarraba malaman firamare guda 33,000, mun ba su jabawar aji hudu kuma mu ka ce sai sun samu a kalla kashi 75 bisa 100, amma saidai ina bakin ciki cewa malamai kashi 66 bisa 100 sun fadi.
''A da, an yi amfani da siyasa wajen daukar malamai aiki, amma muna da niyyar sauya hakan ne ta hanyar kawo malaman faramari matasa kuma wadanda suka cancanta, don dawo da martabar ilimi a jihar,'' a cewar gwamnan.


Malam el-Rufa'i ya jaddada cewa za a tura malamai wurare daban-daban a fadin jihar don daidaita yawan dalibai da malamai.
Gwamnan ya ce dukkan daraktocin gwamnatin jihar za su mayar da 'ya'yansu makarantun gwamnati daga shekara mai zuwa, a wani kokari na ganin an inganta tsarin ilimi.
Jami'in Bankin Duniya, Kunle Adekola, ya nuna godiya ga jihar kan yadda take zuba jari a bangaren ilimi da kuma fifiko da ake bai wa yara mata.
Ya kuma ce Bankin zai zuba jari na kimanin miliyan 30 a makarantar firamari ta Rigasa, wadda ta ke da yawan dalibai 22,000, a matsayin wani bangare na goyon bayan kokarin jihar.
NAN ya ruwaito cewa, Shirin Tallafawa Illimi na Bankin Duniya na taimakawa kusan jihohin arewacin kasar 13.
Harkar ilimi a NAjeriya al'amari ne da aka dade ana kokawa kan tabarbarewarsa, musamman ma a arewacin kasar.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"