Neymar ya taya Messi murnar zuwa Rasha

Ku Tura A Social Media


Neymar na Brazil ya fito ya bayyana farin cikinsa akan nasarar da Argentina ta samu na zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a badi a Rasha.

Neymar ya ce ya yi farin-ciki ne saboda abokinsa Messi, wanda ya ci dukkanin kwallaye uku da Argentina ta doke Ecuador, kuma nasarar da ta ba kasar damar zuwa Rasha a badi.

Brazil ma ta taimakawa Argentina a jiya bayan ta doke Chile ci 3-0.

Neymar ya ce duk da cewa yana da abokanai a Chile amma ya zama dole su taka leda domin abin da suka sa gaba shi lashe dukkanin wasaninsu.

Kwallayen da Messi ya ci a jiya ya ja hankali a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ta cewa Argentina ta dogara da dan wasan ne domin tsallakar da ita zuwa Rasha.

Da farko Ecuador ta razana Argentina inda da soma wasa cikin dakika 40 suka jefa kwallo a raga. Daga bisani ne kuma kafin minti 20 Messi ya farke kwallo tare da sake jefa wasu guda biyu.

Nasarar da Messi ya samu na zuwa ne bayan fargabar ko ba zai je Rasha ba, haka kuma ya jagoranci Argentina ga nasara a daidai lokacin da abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo ya jagoranci Portugal ga nasarar zuwa Rasha a badi bayan doke Switzerland.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"