Mafi Yawan Jami'an Tsaranmu Na Zubar Da Mutuncin Nigeria A Kan Hanyoyinmu:Dr Ibrahim Jalo Jalingo

Ku Tura A Social Media
1. A yau Juma'an nan 13/10/2017 na saurari wata hirar da BBC sashin Hausa ya yi da wani bawan Allah mai nuna kishin kasa mai suna Comrade Abubakar Usman Chairman na Progressive mince for development initiative, inda ya yi ta kukan irin yadda jami'an tsaronmu suke ta lalatar da kansu, suke kuma kaskantar da kasarsu, suke ta karban rashawa ko kuma dai mu ce suke ta kwace wa talakawa masu ababan hawa a kan manyan hanyoyinmu 'yan kudadensu da sunan na goro! Lalle wannan nau'i ne na cin amanar Kasa!

2. Ni kai na shaida ne na ganin ido na adadi mai yawan gaske a kan irin yadda sojojinmu da ke kan check points, da kuma 'yan sandanmu da ke kan check points ko kuma a kan hanya kawai a kan irin yadda wadannnan jami'an tsaro namu babu jin tsoron Allah babu kuma jin kunyar 'yan kasa suke ta zubar da mutuncin Nigeria, suke ta zubar da mutuncin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, suke ta zubar da mutuncin kayan sarki da suke sanye da shi; ta hanyar karban rashawa ko dai mu ce yi wa talakawa mara karfi kwacen dan kadan din da ke hannayensu. Wallahi a duk lokacin da naga wani jami'in tsaro cikin uniform a kan hanya ya mika hannunsa zuwa ga wani miskinin direba yana karban wasu 'yan kudi sai in ji kamar wani mashi ne aka soka mini a kirjina.

3. Lalle muna yin kira cikin girmamawa ga Mai girma shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Haka nan muna yin kira ga gwarzo Chief of Army Staff Lieutenant General Tukur Yusuf Buratai. Haka nan muna yin kira ga mai girma Inspector General of Police (IGP), Ibrahim Idris da cewa don Allah su kara sanya idanu a kan abin da sojojinmu ke aikatawa a military check points da muke da su a kan manyan hanyoyinmu. Su kuma sanya ido a kan abin da 'yan sandanmu ke yi a kan manyan hanyoyinmu. Tabbas wadannan jami'an tsaro da irin wannan mugun hali nasu suna cin amanar da Al'ummah ta danka musu ne.

Allah muke roko da Ya tsarkake kasarmu daga irin wadannan batagarin jami'an tsaro. Ameen.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"