Macen Da Ke Da Wuyar Samu A Yau ----- Sheikh Aminu Ibrahiim Daurawa

Ku Tura A Social Media
Ya kamata mu sani cewa mace daya ce a duniya take da wuyar samu, amma idan ka samu irinta, kada ka kuskura ka rabu da ita. Ya halatta ka auri mace fiye da daya, amma ka sani, mace daya ce kawai, ta ke yin tasiri a rayuwa,  wacce ranka kullum zai kasance a kanta.
Babbar tambaya a nan ita ce, wacece wannan dayar? Ita ce wadda duk da namiji yake muradin samu a rayuwarsa, Ita ce wadda ke koyi da rayuwar shugabar matan duniya kuma diya ga Rasulallahi (SAW), wato Nana Fatima (Allah Ya kara mata yarda).
Haka kuma ita ce wadda kowace mace take fata ta zama. Ga siffofinta guda goma, kamar.
haka:

1. Matar da ta yarda ita mace ce, don haka ta tanadi duk abin da ake bukata a wajan mace.
2. Mace mai hikma da azanci, wacce ta karanci mijinta da kyau, kuma take kaucewa duk abin da  zai haddasa matsala a tsakaninsu.

3. Mace mai taushin hali da nutsuwa, wacce miji yake jin nutsuwa, idan yana tare da ita.

4. Mace da kudi bai dame ta ba, ita mijinta kawai take so, ko da akwai ko babu.

5. Mace mai hakuri da juriya, babu gunaguni, babu mita, da kai kara ga iyaye ko kawaye.6. Macen da ta dauki kanta likita, mijinta mara lafiya, domin ya sami kulawa, ta musamman da. riritawa.

7. Mace mai saurin daukar ishara, tana gane shiru da magana, da motsi da yanayin shigowa da  fita, samu da rashi da kuma yanayin da ake ciki a duniya ko a gari.

8. Mace mai sakakkiyar zuciya, mara kulli da ramuwa.

9. Mace mai karawa miji kuzari da karfin hali, a kan kyawawan manufofinsa.

10. Mace mai rikon amanar aure, da soyayya ga mijinta kawai.

Sources:www.darulfatawa.com

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"