Honarable Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice

Ku Tura A Social Media


Fitaccen dan majalisar wakillan nan na Najeriya mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, 'Yankwashi da kuma Gwiwa dukkan su a jihar Jigawa dake a Arewa maso yammacin Najeriya mai suna Honarable Muhammad Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice.

Shahararren dan majalisar dai ya yi wannan caccakar ne a yayin da yake tsokaci a zauren na majalisar game da sabon tsarin nan na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari din da ke fitar da doyar da aka noma zuwa kasashen ketare.

NAIJ.com dai ta samu cewa ta yake tsokacin, Alhaji Gudaji Kazaure ya nuna rashin dubara da kuma sanin ya kamata daga bangaren gwamnatin game da wannan tsarin inda yace shi baiga yadda za'ayi talaka ya mori wannan irin bahagon tsarin ba na fitar da kayan abinci zuwa kasashen waje sannan kuma an hana shigowa da shi.

Dan majalisar daga karshe sai ya jawo hankanin shugabannin majalisar yan uwansa da ma sauran shugabannin kasar a dukkan matakan mulki da su duba wannan matsala domin kawo gyara.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"