Ban yi nufin kunyata Atiku Abubakar ba, in ji tsohuwar surukar sa

Ku Tura A Social Media


- Tsohuwar surukar Atiku Abubakar, Ummi Bukar Bolori, ta ce ba ta da nufin kunyata Atiku

- Ta yi wannan bayani ne saboda rigimar su ta kula da 'ya'ya tsakanin ta da tsohon mijin nata Aminu

- Ta ce tsohuwar sarakuwar ta Titi ce silar rigimar kuma tsohon mijin na ta ya yi mata tinkahon babu wanda ya isa ya ja da su

Ummi Bukar Bolori, Tsohuwar matar dan Atiku Abubakar wato Aminu, ta yi bayani dalla-dalla a kan abun da ya janyo rigimar su na neman izinin ganin 'ya'yan su, Amirah da Aminu.

Ummi ta bayyana wa Jaridar Punch yadda har sau biyu ta na neman sasantawa ta hannun Atiku cikin ladabi da 'ya take yi wa mahaifin ta. Ta ce ta na tunanin ko shi Atikun ba zai goyi bayan dan sa ba bisa ga fallasar lamarin.

A cewar ta, ta bi duk wata hanyar lumana da sirri da ya kamata ta bi amma lamarin ya ci tura. Ta ce ba a son ran ta bane ake cikin halin da ake yanzun.Ummi ta zargi matar Atiku, Titi, da fallasawa al'umma halin da a ke ciki ta hanyar hana ta kasancewa tare da 'ya'yan nata. Ta ce shi tsohon mijin nata da kan sa ya fada mata uwar sa ce ta umurce shi da ya hana ta ganin 'ya'yan nata.

Ta ce har fada mata ya yi cewan babu wanda ya isa ya ja da su. A cewar ta, akwai ma wani lokaci da Titi ta fada wa DPO ya kama ta saboda ta je ganin 'ya'yan nata a makaranta. Ta kuma ce Titi na mata hakan ne saboda jin zafin rabuwa da dan ta da ta yi.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"