Abubuwa Uku Dake Birgeni A Kannywood, Da Uku Dake Ci Mini Tuwo A Kwarya -Fati SU

Ku Tura A Social Media

Shahararriyar ‘yar wasan fina-finan Hausa Fati SU ta yi hira da gidan labaran Premium Times Hausa inda ta ce akwai wasu abubuwa guda uku da ke burgeta a farfajiyar Kannywood da wasu guda uku da ke ci mata tuwo a kwarya yayin shirya fim.
A yayin hirar, Fati SU ta yi matukar jinjina wa jaruman kannywood da sauran yan uwanta da ke harkar fina-finai a farfajiyar.

Ta shaida mana wadansu ababe uku da ke matukar burgeta a farfajiyar.
1 – Taimaka wa juna. Idan Har kana wannan farfajiya na Kannywood zaka ga ana tattaimaka wa juna musamman idan kai sabon shiga ne. Ana amfana da haka mussamman daga wurin dadaddu a harkar.

2 – Rashin yi wa juna bakin ciki. Ko da yake kowa da yadda yake ganin abin, ni dai a nawa ganin sai dai a sami rashin jituwa amma son juna ya fi yawa a tsakanin mu. Rashin bakin ciki ga juna musamman idan baka dade ba da Fara harkar. Manyan za su yi ta taimaka maka kaima tauraron ka ya shana.

3 – Hadin Kai – Duk inda kaga dan wasa to zaka ga ana tafiya tare ne. Ko da akwai na ciki amma dai ana tare.

Uku dake ta da mini hankali
1 – Tilasta maka sai ka kware – Duk da abune mai kyau amma gaskiya wata rana sai kaji kaman ka sa Ihu idan Direkta ya matsa sai kayi yadda ya kamata.
2 – Idan an hada ka da jarumi ko Jaruma a wasa, musamman idan yana gaba da kai sai kaji kamar ba ka komai saboda kwarewarsu. Sai dai yana da amfani domin shima hakan gwaji ne.
3 – Idan wurin da za ayi fim din ba dadi sai kaga ka kosa a gama fim din kaje ka huta.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"