Yadda Hukumar Kwastan Ta Sake Kama Bindigogi Fiye Da Dubu Daya

Ku Tura A Social Media


Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya, kwastam, mai kula da shiyyar tashar jiragen ruwa ta Tincan Island da ke a Legas a kudancin kasar, ta kama manyan bindigogi sama da dubu daya.

Shugaban hukumar kustom na kasa kanar Hamid Ali mai ritaya, shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Litinin. Ya kara da cewa an shigo da bindigogin ne daga kasar Turkiya.

Bindigogin sama da 1,000 dai kamar yadda shugaban hukumar kostom ya nuna, ko wacce daya tana iya hallaka mutane da dama a cikin lokaci guda. Koma baya da sauran bindigogi.
Hukumar ta gano cewa bindigogin ana yi musu dure ne da harsashi -- to sai dai ya ce hadarinsu ba ya misaltuwa.

Idan dai ana iya tunawa wannan shi ne karo na uku da rundunar kwastam ta kama bindigogi kusan kira daya. Kuma al'amarin kamen bindigogin ya zama kusan a ko wanne sulusi a wannan shekara. Bindigogi da aka kama a sulusin farko a wannan shekara dai an shigo da su daga China sai kuma na biyu da na uku aka shigo da su daga kasar Turkiyya.
Za mu sa kafar wando daya da masu karya doka - Kwastam

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"