Kalaman Gwamna El-rufai Sun Jawo Za A Yi Addu'a A Jihar Katsina Kan Rasuwar Yar'adua

Ku Tura A Social Media

A yau Juma'a ne aka shirya gabatar da gagarumar addu'a bayan sallar Juma'a a kowane masallacin Juma'a da ke fadin jihar Katsina kan zargin rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa 'Yar'Adua.

Ustaz Muhammad Sada na Kungiyar Matasa Musulmi, reshen jihar Katsina wanda ya bayyana wannan kudirin, ya ce,  wannan addu'a za a yi ta ne a duk masallatan Izala da Darika da ke fadin jihar Katsina.

Ya kara da cewa, babban makasudin yin wannan addu'a shine akan kalaman da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya furta game da rasuwar marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa 'Yar Adu'a.

A wani bangaren kuma wata kungiyar mai rajin hadin kan matasan Jihar Katsina ta shirya wata zanga-zanga a kowace ranar Juma'a idan har Gwamnatin Tarayya ba ta dauki wani mataki ba akan kalaman Gwamna El-Rufa'i ba.

Shugaban kungiyar Alhaji Sabi'u Tanko Safana ya ce, mutanen Jihar Katsina har yanzu suna cikin bakin cikin rashin 'Yar Adua kuma ba su ji dadin kalaman Gwamna El-Rufa'i ba.

"Mun yi tunanin gwamnan Jihar Katsina zai mayar wa takwaransa Gwamna El-Rufa'i raddi amma muka ji shiru." In ji Shugaban matasan.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"