Jaruma Hadiza Gabon Ta Soma Fitowa A fina-finan Nollywood

Ku Tura A Social Media

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.Jarumar ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ta fara gwada sa'arta a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin fina-finai a bangarori daban-daban.
A cewarta, "Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a gajerun fina-finan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.


"Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna 'Lagos real fake life'.
"Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin 'yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim.

Hadiza Gabon ta kara da cewa "Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al'adata ba".
Jarumar ta ce babu wani "bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji dadin soma fitowa a fina-finan Nollywood".
BBCHausa.Com

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"