Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Hana Mabiya Darikar Shi'a Kowane Irin Taro A Jihar

Ku Tura A Social Media
Kwamishinan Shari'a na jihar Sokoto Barista Sulaiman Usman (SAN) ne ya zayyana haka a lokacin da ya gudanar da taron ga manema labarai a Sokoto, bayan wani zama da shugabannin jami'an tsaro na jihar Sokoto don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Kwamishinan ya ce " Akwai wasu shirye-shiryen taruka da mabiya Darikar Shi'a (IMN) suke yi yanzu haka a jihar Sokoto wanda ake hasashen za su iya tada zaune tsaye a jihar Sokoto, wanda idan ba a dauki mataki ba wadannan shiriruwa da 'yan Darikar Shi'a za su gudanar za su iya haifar da rashin zaman lafiya a jihar Sokoto".

Ya kara da cewa " A dalilin haka Gwamnatin Jahar Sokoto ta hana kowane irin Taro ko shirin wani taro na yan Darikar Shi'a a Jahar Sokoto don wanzarda zaman lahiya". Inda Kwamishinan ya cigaba da cewa " Duk wani wanda ya taka wannan dokar to yayi kuka da Kanshi ga abunda hukuma zata dauki mataki gareshi domin shi ya jama kansa.
Daga karshe Shugaban 'yan' sanda na jihar Sokoto , Muhammad Abdulkadir ya yi kira ga 'yan Darikar Shi'a da su guji kowane abu da zai iya haifar da tashin hankali a jihar Sokoto tare da janye zaman lafiya da aka san Sakkwatawa da shi.

Saidai wasu na ganin a jihar Sokoto, kamar sauran jihohi mabiya mazahabar suna gudanar da shiriruwan su cikin tsari da jagoranci inda wani lokaci jami'an tsaro ko wasu mutanen gari suke kokarin hana su, daga nan sai abun ya rikice zuwa fadace -fadace.
A bangaren mabiya mazahabin Shi'a sun ce an buge su an hana su kuka, domin bayan kisan gilla da kone dukiyoyin da aka yi masu a kwanan baya, yanzu kuma ana cewa sune ke kawo rikici ga abinda suka share sama ga shekara ashirin suna yi.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"