FIFA ta fitar da sabon tsarin jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya

Ku Tura A Social Media
Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce zata yi amfani da sabon rahoton da zata wallafa a ranar 16 ga watan Oktoba, na kasashen da suka fi kwarewa a fagen kwallon, wajen tsara jadawalin yadda kasashe da zasu fafata da juna a matakin rukuni na Gasar Cin Kofin Duniya, wadda za'a fitar da jadawalinta a ranar 2 ga watan Disamba.
A cewar hukumar daga yanzu zata rika tsara jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya ta hanyar duba kwarewar kasashe, a maimakon tsara jadawalin bisa nahiya-nahiya.
Karkashin sabon tsarin na yanzu, FIFA ta ce za’a kasa baki dayan kasashe 32 da zasu fafata zuwa kashi 4, kasashe da suka fi kwarewa guda takwas a kashi guda, sai kuma wadanda ke biye dasu a matakin kwarewar, su ma guda takwas a tukunya daya.
Daga kowane kashi kuma za’a rika dauko guda ana hada ta da sauran kasashen da suke a mataki daban daban wajen shahara.
FIFA ta ce makasudin haka shi ne tabbatar da cewa kowane rukunin Gasar Cin Kofin Duniyar ya samu adalci wajen hada kwararru da wadanda ke biye da su.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"