Farare Da Kyawawan Mata Ake Sawa A Fim Yanzu inji Maryam A Baba (Sangandali)

Ku Tura A Social Media

Maryam A Baba wacce akafi sani da Maryam Sangandali na ɗaya daga cikin mawakan Hausa na zamani da tauraruwarsu ke haskawa a wannan karnin, itama ta halarci taron marubuta na duniya da aka gudanar cikin makon da ya gabata.

Sangandale tace ta zaɓi salon waka cikin ruwan sanyi ne wanda tace hakan ya fi gamsar da masu sauraro tare da nishaɗantar da masu sauraro.

Da aka tambayeta ko me ne dalilin da ako da yaushe akafi ganinta da Aminu Alan waka, sai ta amsa da cewar “ko shakka babu fahimta ce tazo ɗaya dashi, musamman idan aka dubi shima irin salon rera wakarsa kenan, kuma yana taimakamin wajen gyaramin wakokina tare da yimin gyara, wani lokaci ma ya rubuta min yace ga yadda wakar zata kasance. Wannan tasa ake ganin muna Kamanceceniya cikin wakokinmu”. Inji Sangandale

Sannan Maryam A Baba (Maryam Sangandale) ta bayyana cewar tun ina firamare nake sha’awar wakoki, saboda haka na kudurce a zuciyata cewar idan na gama makaranta nima zan bayar da tawa gudunmawar.

Haka kuma an tamabayi Sangandali shin me yasa bata fita a fina-finan Hausa?

Sai ta ce “gaskiya iyaka cina waka kawai, kasan su fim ana ɗaukar kyawawan mata kuma farare ne, to mu da muke haka sai mu tsaya iya wakar kawai.

Akarshe Maryam Sangandali ta bayyana gamsuwarta da wannan taro.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"