Classiq Ga abubuwa 5 game da wannan jarumi mawaki

Ku Tura A Social Media
Shidai wannan mawakin ya ficce a wakokin hausa hip-hop kuma ya shahara sosai a ƙasar domin yadda yake sako baitutukar shi cikin harshen hausaBarnabas buba Luka wanda aka fi sani da “Classiq” jarumi ne a fannin wakar hip-hop.
Ga masu tambaya ko wannan shahararen mawaki dan arewa ne, ku sha kurumin ko domin wannan jarumin dan arewa ne mai asali.

Shidai wannan mawakin ya ficce a wakokin hausa hip-hop kuma ya shahara sosai a ƙasar domin yadda yake sako baitutukar shi cikin harshen hausa.
“Sarki” kamar yadda masoyan shi ke kiran shi yana alfahari da yaren hausa kuma a duk inda ya tsinci kanshi yana tallafa yaren tare da al’adar yan arewa.
Kasancewa yau take ranar haihuwar shi ne ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da shi ;

1. Dan jihar bauchi

Wannan mawakin da aka haifa ranar 21 ga watan Satumba na 1991 haifaffen dan jihar Bauchi ne kuma shine da na karshi cikin yara 3 da iyayen sa suka haifa.

2. Baban shi malami ne

Kwarrai ko kana iya kiran shi da “dan mallam” domin shima na alfahari da haka kasancewa babban shi malami ne a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake nan jihar Bauchi. Baban shi likita ne na boko a fannin ilimin “geography” ita kuma uwar sa malama ce a asibiti.

3. Yayi karatun sa a Arewa

Shidai wannan jarumin waka ya fara karatun sa na firimari garin Bauchi kuma ya kammala karatun digiri dinsa a jami’ar Ado Bayero dake
Kano inda yaa karanta ilimin kwamfuta.

4. Ya yayi wasa a garuruwa da dama kuma jakadan arewa ne

Classiq ko kuma “arewa Mafia” kamar yadda yake ma kansa lakabi yayi wasa a wurare da dama kuma ya yi waka tare shahararrun mawakan
Nijeriya .

5. Duk wakar shi akwai dangantaka da Arewa.

Ko cikin baitutukar shi ko sunnan wakar ko kuma yanayin shigar shi a bidiyo zai ka ji ko ka gan abun da ya ganganci arewa. Duk da cewa wannan mawakin yana iya basaja ya koma wakokin turanci amma ya amince da ya dabbaka yaren ga idon duniya.
yayi wakoki irin su Zauna, Sama, hoto, barka da sallah, Ana haka da dai sauransu.
Daga nan sashen hausa na pulse muna ma wannan jarumin mawaki mai hazaka murna da zagayowar ranar haihuwar shi.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"