Kalli Dandazon magoya bayan shugaban ƙasa Buhari Har Yanzu Muna Tare Da Shugaba Buhari, Cewar Kanawa

Ku Tura A Social MediaDandazon magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis sun gudanar da addu'o'i na musamman ga shugaban kasan a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata cikin birnin Kano don nuna farin cikin su da dawowarsa daga jinya da kuma fatan Allah ya kara masa lafiya.

Daga bisani dandanzon jama'an karkashin jagorancin hadimin shugaba Buhari kan kafafun sadarwa, wato Sha'aban Sharada sun dunguma zuwa fadar gwamnatin Kano, inda gwamna Ganduje ya tarbe su.

Gwamnan ya nuna farin cikinsa game da yadda ya ga dandanzon magoyan bayan shugaban kasan, wanda a cewarsa hakan ya nuna cewa har yanzu al'ummar jihar Kano na tare da shugaba Buhari dari bisa dari 

Kalli hotunan dandazon magoya bayan shugaba muhammad buhari


Ku kasance da www.hausaloaded.com

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"