Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Cafko Barayin Gwamnati Daga Dubai

Ku Tura A Social Media

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a wata yarjejeniyar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda za ta fadada yaki da cin hanci da gwamnatinsa take yi da tsaron kasa da kuma bunkasa tattalin arziki.

Yarjejeniyar ta yi tanadin musayar mutanen da suka aikata manyan laifuka tsakanin Najeriya da Hadaddiyyar Daular Larabawa. Shugaban ya bayyana al'amarin da wani muhimmin ci gaba ga kasar wanda zai taimaka wajen bunkasar tattalin arziki da tsaro da yaki da cin hanci da ciki da wajen kasar.

Sabuwar yarjejeniyar za ta taimaka wajen tasa keyar wadanda aka samu da laifin aikata cin hanci a kasashen biyu. Ya ce an jinkirta fara aiki da cikakkiyar yarjeniya ne saboda bangarorin biyu ba su kammala cimma matsaya ba.

"Wannan yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma zai taimaka wa hukumomin kasashen wajen gurfanar da wadanda aka samu da aikata laifin cin hanci da rashawa," in ji Shugaba Buhari. Sauran batutuwan da shugaban ya zartar a ranar Alhamis har da wata yarjejeniya da ta shafi yankin Tafkin Chadi da Kamaru da Janhuriyar Tsakiyar Afirka da Libya da kuma Jamhuriyar Nijar.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"