Saboda Neman Kudin Makaranta Na Fara Kera Bindiga.!!!..Cewar Wani Matashi

Ku Tura A Social Media


Daga Habu Dan Sarki

Wani matashin yaro mai kimanin shekaru 19 mai suna Eric Labari, wanda dake karamar hukumar Mangu a Jihar Filato ya shiga hannun jami'an tsaro a Jos, bayan da wani yaro da aka kama da bindiga kirar gida ya fallasa harkar da suke yi.

Bayan da jami'an tsaro na sojojin rundunar hadin gwiwa ta Operation Safe Haven suka kafa wani matashin yaro mai suna Benshak Nandong dauke wata bindiga da aka yi ta da fasahar gida, sun tuhume shi don sanin wanda ya kera masa da kuma yadda ta isa hannun su. Shi kuma ya bayyana musu yadda wannan matashi Eric yake samsana'o'da bindigogin da suke amfani da su wajen aikata laifuka.

Bayan gano lungun da Eric Labari yake sarrafa masana'antar kera bindigogi a garin Mangu, jami'an rundunar ta Operation Safe Haven sun kai shi Jos, inda suka bincike shi, don sanin inda ya koyi wannan sana'ar.

Abin da suka gano daga Eric shi ne an kore shi a makarantar da yake karatu, wato makarantar koyar da sana'o'i ta garin Bukur, inda ake koyar da kere-kere da sarrafa karafa, saboda ya gagara biyan kudin makaranta.

Wannan dalili ne, a cewar sa wata dama da ta sa ya shiga amfani da basirar da Allah ya yi masa, don ya samu ya tara kudin da zai koma makaranta.

Babban kwamandan rundunar hadin gwiwa ta OPSH Manjo Janar Rogers Nicholas ya yi takaicin halin da wannan yaro ya samu kansa a ciki, wanda ya ce Allah ne kadai ya san yawan mutanen da suka yi amfani da makaman da yake kerawa.

Har kawo hada wannan rahoton, Eric Labari  yana tare da jami'an tsaro ana gudanar da bincike kafin a mika shi ga jami'an 'yan sanda, wadanda za su tura shi kotu gaban kuliya manta sabo.

©Zuma Times Hausa

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"