Rahama Sadau Zata Gana Da Priyanka chopra

Ku Tura A Social Media

Fitacciyar Jarumar Masana’antar shirya Fina-finan Bollywood Priyanka Chopra na fatan haduwa da Jarumar Fina-finan Hausa ta Kannywood Rahma Sadau a dan wani lokaci kadan mai zuwa.

Tun farko Jaruma Rahama Sadau ce ta aika da sakon bankadar mafarkinta a fejin Priyanka na Twitter kan irin mafarkin da take da shi na kasancewa kamar Jaruma Chopra. Sakon wanda Jarumar ta rubuta kamar haka “Idan na duba nasarar da kika cimma, tana bani karin gwiwa na zama kamarki” – inji Sadau zuwa ga Chopra.

Sadau ta samu amsar kalmominta ‘yan dakikoki kadan daga Chopra wadda ta ba ta alwashin cewar “Ina godiya Rahama Sadau. Ina Fatan haduwa da ke nan gaba. Fatan alheri da kauna kan komai” – Inji Jaruma Priyanka Chopra.

https://t.co/eDG6xwAgGi

https://t.co/5a0ehF6xXg

Jaruma Sadau ta nuna murnarta matuka kan samun wannan amsa tare da ayyana cewar tana nan tana jiran lokaci. Sadau dai ta dade da kaunar wannan jaruma a ranta, wanda har ta kai ana mata lakabi da sunan Jarumar wato Priyanka Chopra ta Kannywood

©arewamobile.com

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"