Barayin Gwamnati Ne Suka Kafa Boko Haram Da 'Yan Tawayen Biafra, Cewar Magu

Ku Tura A Social Media
Barayin Gwamnati Ne Suka Kafa Boko Haram Da 'Yan Tawayen Biafra, Cewar Magu

Daga Aliyu Ahmad

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) wato Ibrahim Magu ya bayyana cewa barayin da suka wawushe dukiyar kasar nan a shekarun baya su suka kirkiro kungiyar masu fafutular kafa yankin Biafra.

Magu ya bayyana hakan ne a jiya Juma'a a yayin taron da suka gudanar a Kano. Magu ya kara da cewa idan ana so kasa ta ci gaba, ya zama wajibi 'yan Nijeriya su yaki rashawa a ta kowane fanni.

"Cin hanci da rashawa babbar barazana ce ga hadin kan kasar nan kuma dole ne mu yake ta duk da kalubalen da muke fuskanta.

"Barayin gwamnati su suke daukar nauyin masu fafutukar kafa yankin Biafra da kuma kungiyar Boko Haram.

"A shirye barayin gwamnati suke da su ci gaba da daukar nauyin rikice-rikicen dake aukuwa domin su kawo rudani saboda a kau da hankali akansu. Amma ba za su yi nasara ba.

"Ina mai tabbatar muku da cewa shugaban kasa da mataimakinsa sun sha alwashin yakar rashawa, kuma za mu ci gaba da yakar rashawa a kasar nan.

"Haka kuma, wadanda suka wawushe dukiyar kasarmu ba su kai su dubu goma ba, don haka bana tunanin wadannan mutane za su rinjayi mutane sama da milyan 150 dake kasar nan", cewar Magu.

©facebook/Rariya

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"