Mawaki Ado Gwanja Ya Sha Duka A Hannun Jami'an 'Yan Sanda Na Kano

Ku Tura A Social Media
Mawaki Ado Gwanja Ya Sha Duka A Hannun Jami'an 'Yan Sanda Na Kano  

Daga Habu Dan Sarki

Fitaccen mai wasan barkwancin nan kuma mawakin Hausa wanda aka fi sani da Ado Gwanja ya sha kashi a hannun wasu fusatattun jami'an 'yan sanda dake aiki tare da caji ofis na 'Yan Akwa dake cikin birnin Kano, inda ya je domin belin wani yaron sa da aka kama.

Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne sanadiyyar hayaniyar da ta kaure tsakanin Gwanja da 'yan sandan bayan da suka nemi ya biya naira dubu 10 domin belin yaron nasa, inda  shi kuma mawakin ya kafe kan ba zai bayar ba, domin kuwa ya san beli kyauta ne.

Jin hayaniyar dake faruwa tsakanin maigidansa da 'yan sandan dake tsare da shi, a cewar wani jami'i da al'amarin ya faru kan idanunsa, sai yaron Gwanjan da ake tsare da shi bisa laifin yawon dare, mai suna Chassis ya sa baki don a hayaniyar da ake yi don kare mutuncin maigidan sa, abin da ya haifar masa da hucewar fushin 'yan sanda a kansa.

Shi ma Gwanja da ya ga dukan ya wuce misali sai ya shiga tsakani domin ya kwaci yaronsa, ai kuwa sai suka hada da shi suka lakada musu dukan kawo wuka.

Yanzu haka dai lamarin na gaban kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, yayin da ake tsare da dan sandan da ya haifar da wannan danyen aiki a hedkwatar 'yan sanda dake Shahuci.

©Zuma Times Hausa

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"