Mai horar da yan wasan Najeriya ya bukaci Ahmad Musa da sauran musulmai su aje azumi

Ku Tura A Social Media


Mai horar da 'yan wasan Super Eagles, Gernot Rohr ya bukaci Ahmed Musa da wasu 'yan wasa musulmai na kungiyar da su ajiye azumi a yayin wasan da za su kara da kasar Afrika ta kudu.

Saidai 'yan wasan da lamarin ya shafa irin su Ahmed Musa, Abdullahi Shehu, Alhassan Ibrahim da Abdullahi sun ki amincewa da hakan inda suka bayyana cewa babu yadda za a yi su ajiye azumi saboda wasan kwallo.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Najeriya dai za ta kara da kasar Afrika ta Kudu ne a ranar 10 ga watan da muke ciki, a filin wasa na Ibadan babban birnin jihar Oyo a wasan share fagae na cin kofin kasashen Afrika.


A wani labarin kuma Tsohon dan wasan Newcastle na tsakiya Cheick Tiote ya rasu yana da shekara 30 bayan ya fadi a lokacin da yake atisaye da kungiyarsa ta China Beijing Enterprises.

Mai magana da yawun dan wasan Emanuele Palladino ne ya tabbatar da mutuwar tasa a ranar Litinin din nan.

Cheick Tiote ya yi wa kasarsa Ivory Coast wasa inda suka dauki kofin kasashen Afirka na shekara ta 2015.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"