Kannywood: Hukumar Moppan Zata Hukunta Sulaiman Bosho

Ku Tura A Social Media
HUKUMAR MOPPAN ZATA HUKUNTA SULAIMAN BOSHO.

Daga Haruna Sp Dansadau.

Kungiyar ladabtar da jarumai maza da mata Moppan ta fitar da wata sanarwa a safiyar Jiya talata cewa: zata hukunta jarumin barkwanci Sulaiman Bosho bisa laifin dori akan abinda darakta ya umarce shi wato over role kenan.

Acewar Moppan: “Mun jima muna ganin kura kuran da Bosho Yake Yi acikin fim, mun kira shi dan ya gyara amma ya kasa gyarawa.” “Mun tuhumi daraktocin da suke da suke sa shi acikin fim amma sunce, su basu ga laifi ko munin kalamansa ba.

Dan hakane muka yanke hukuncin hukunta daraktocin da kuma shi jarumi Bosho”. Inji Moppan. Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa hukuncin da za’ayi jarumi Bosho akwai tara wanda aka ci Bosho dan wannan ya zama izna agare shi dama daraktocin da suke bashi umarnin furta kalaman da basu dace ba.

Da muka tambayi Bosho akan da wacce fuska ya kalli wannan hukunci? Sai ya amsa da cewa: “Wannan hukunci son ransu suka aikata, domin mutane sune ya kamata su gane laifin da muka aikata basu ba, domin mutane sune masu kallon mu, sune alkalai ba Moppan ba.”

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"