'Ban ga dalilin ƙarin kuɗin aikin hajjin bana daga Nigeria ba''-Bbc hausa

Ku Tura A Social Media

Wasu kamfanonin jigilar alhazai a Nijeriya sun ce idan aka yi ƙididdiga sosai a kuɗin kujerar da hukumar alhazan ƙasar ta sanar a bana. za a iya samun rangwamen kimanin naira dubu 500 a farashin aikin hajjin bana,
Hukumar alhazan dai ta sanar da kuɗin kujera wanda ya haura naira miliyan ɗaya da dubu 500 a kan kowacce kujera, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar.

Kuɗin aikin hajji ya yi tashin da bai taɓa yin irinsa ba a Nijeriya ba, inda aka samu ƙarin kimanin kashi 50 cikin 100 a kan kujera.

Hukumar alhazai ta Nijeriya ta ɗora alhakin ƙarin wanda wasu ke cewa zai hana masu ƙaramin ƙarfi zuwa sauke farali a ƙasar Saudiyya, a kan tashin kuɗaɗen musayar waje.
Sai dai, wani mai kamfanin shirya zirga-zirgar jiragen sama na 'Darma Air Services' da ke Kano, ambasada Usman Darma ya ce kamfanonin gida za su iya jigilar alhazan Nijeriya a kan naira dubu 900 idan gwamnati za ta yi tattaunawar fahimta da su.
Ya ce ana iya samun mafita kan abubuwan da ke sanya kujerar aikin hajji yin tsada idan an bi diddigi, matuƙar gwamnati za ta ɗauki matakai da wuri.
Ambasada Darma ya yi misali da farashin jirgin da za a dauki alhazan Nijeriya cewa za a iya samun jirgi wanda farashinsa bai wuce dala 500 ba.

Sannan ya ce idan ana batun masauki a biranen Makka da Madina, za a iya samarwa kowanne maniyyaci ragin kimanin dala 200.
"Ai ana maganar gado ne ba ɗaki ba ga kowanne maniyyaci, don haka za a iya samun rangwame sosai. Ina mai tabbatar da cewa kamfanonin gida za su iya ɗaukar kowanne maniyyaci a kan dala dubu ɗaya zuwa Saudiyya, ƙasa da naira dubu 400."
Darma ya yi misali da cewa ana ɗaukar 'yan ƙasar Pakistan zuwa Saudiyya don aikin hajji a kan dala dari tara, kuma Nijeriya tafi kusa da Saudiyya idan an kwatanta da Pakistan.
A cewar mai harkar jigilar matafiyan wuraren da ake saukar da alhazan Nijeriya a ƙasa mai tsarki, sukan kasance masu nisan gaske daga Harami, kuma a ajiye mutum uku zuwa biyar a ɗaki ɗaya, don haka bai ga dalilin da zai sa a kasa samun rangwame ba.

"Idan aka bi kididdiga za a iya sama wa alhazan Nijeriya masaukin da bai gaza dala dubu ɗaya ba."

Ya ce: "Mun fada wa hukumar alhazai cewa wannan kuɗi da suka sanya ya yi yawa, don haka ya kamata gwamnati ta kafa wani kwamiti mai ƙarfi da zai duba aikin hajjin bana.

Don kuwa, za a iya gyarawa tun lokaci bai kure ba."

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"