Ba Laifin mu bane ya sa kudin Aikin Hajji yayi tashin gwauron zabo

Ku Tura A Social Media
Ba Laifin mu bane ya sa kudin Aikin Hajji yayi tashin gwauron zabo

Faduwar darajar Naira ce sila-NAHCON

Daga Ibrahim Baba Suleiman 

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana dalilan da suka sa aka samu karin kusan kashi 50 bisa dari a kudin kujerar aikin hajjin bana a kasar.

A makon nan ne hukumar ta bayyana yawan kudaden kujera a bana wanda ya nuna kudin kujera mafi karanci shi ne sama da Naira miliyan daya da rabi.

Hakan dai ya sa wasu maniyyata da dama a Nijeriya yanke kaunar sauke faralin a bana.

Shugaban hukumar Alhaji Abdullahi Mukhtar Muhammad ya ce, karin ya tsaya a kashi hamsin bisa darin ne ma saboda rangwamen da gwamnatin kasar ta yi wajen yi wa maniyyatan canjin dalar Amurka.

Alhaji Abdullahi Mukhtar Muhammad ya kara da cewa, faduwar darajar Naira shi ne ginshiki na karuwar farashi, duk kuwa da rangwamen da gwamnatin kasar ta yi.

Shugaban hukumar aikin Hajji ta Najeriyar ya kara da cewa a wannan karo an samu raguwar Dala dari uku a kudin da alhazai ke biya na masauki da kuma kudin jirgi.

A bara dai maniyyata daga arewacin kasar sun biya Naira 998,248.92 a karamar kujera, wasu kuma sun biya Naira 1,047,498.92 na matsakaiciyar kujera, kana masu babbar kujera sun biya Naira 1,145,998.92.

Su kuma maniyyata daga kudancin kasar sun biya Naira 1,008,197.42, su kuma masu matsaikaiciyyar kujera kuma sun biya N1,057,447.42, inda masu babbar kujera suka biya Naira 1,155,947.42.

A bana an soke wannan tsarin kujeru daki-daki, inda aka mayar da shi na bai daya, kuma kowane maniyyaci zai biya abin da jiharsa ta kayyade.

A bana an tsayar da guzurin bai daya na dala 800 na Amurka.

Idan baku manta ba, shugabannin addini
sun fara kira ga Gwamnatin tarayya da su shigo cikin lamarin domin samun yadda talaka zai samu rangwame, inda Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah Wa'Ikamatis Sunnah a Naijeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi kira ga Gwamnatin Nijeriya ta bada tallafi na musamman domin sassauta kudin aikin hajjin bana, wanda al'umma da dama suka shiga dahuwa domin tashin farashin kujerar.


Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"